Shirin Horarwa na Duniya na Beiersdorf BEYOND 2026
An buɗe neman shiga cikin Shirin Horarwa na Duniya na Beiersdorf BEYOND 2026. A matsayin me neman horo a ɓangaren Supply Chain (Tsarin Samarwa da Rarrabawa), za ka samu damar koyon fannoni daban-daban a cikin kamfanin FMCG mai saurin tafiya da ci gaba.
A cikin ayyuka daban-daban, za ka samu cikakkiyar ƙwarewa da fahimta kan harkokin gudanarwa da dabarun supply chain, tare da faɗaɗa iliminka ta hanyar aiki da sassa daban-daban na kamfani.
Kuma kaima kanada gudun mawar da zaka iya bayarwa domin cigaba. Za ka taimaka wajen tsarawa da aiwatar da hanyoyi da tsarin da za su ƙarfafa ingantaccen supply chain mai dacewa da bukatun gaba, wanda zai amfani kamfani, kwastomomi da abokan hulɗa.
Tun daga ranar farko, za a ba ka dama ka ɗauki nauyin aiki tare da taimakawa wajen tsara makomar kamfanin.
Abubuwan da ake Bukata
Masu neman shiga dole su kasance suna da:
Digiri na jami’a (Bachelor ko Master) a:
Supply Chain Management
Industrial Engineering
Logistics
Business
Ko wani fanni mai alaƙa
Kwarewar jagoranci da iya ɗaukar nauyi tare da aiki tare da mutane
Sha’awar harkokin supply chain da inganta ayyuka
Ƙwarewar nazari da amfani da fasahar zamani tare da tunani mai tsari da warware matsala
Sauƙin mu’amala, iya sadarwa, aiki tare da mutane da kuma ɗaukar mataki
Sha’awar jagorantar ayyukan supply chain
Son haɗa bayanai, tunanin tsari da kirkire-kirkire domin inganta aikin supply chain
Aƙalla watanni 6 na ƙwarewar aiki ta hanyar internship ko makamancin haka
Cikakken Bayanin Shirin
Za a fara shirin horarwar BEYOND ne a watan Satumba 2026
Fa’idodin Shirin
Samun ƙwarewar aiki a kamfani na duniya
Aiki tare da ƙungiyoyi na duniya, yanki da ƙasa
Gina ƙwarewa a bangaren supply chain
Damar haɓaka sana’a da samun gogewa mai amfani
Samun damar jagoranci da koyon dabarun aiki na zamani
Wannan damar tana da fadi sosai saboda haryanzu ba a sanar da ranar rufewa ba
A karshe
Wannan shiri dama ce mai girma ga matasa masu sha’awar supply chain da harkokin gudanarwa domin samun gogewa a kamfani na duniya. Idan kana da ilimi, ƙwarewa da sha’awar ci gaba a wannan fanni, wannan na iya zama babbar dama gare ka.
.jpeg)
Post a Comment